
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa tsohon shugaban sojojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas mukamin kula da gudanar da jihar rivera bayan da ya dakatar da Gwamna Fubara.
A ranar 18 ga watan Maris ne dai shugaban kasar ya dakatar da gwamna Simi Fubara da mataimakinsa da majalisar jihar na tsawon watanni 6 kamin aga abinda hali yayi.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa, sojoji sun yiwa Gwamna Fubara daurin talala a gidansa tare da iyalinsa.