
ina Bin Atiku Abubakar Bashi Naira miliyan 15 yakasa Binaya, Wani Matashi yayi Barazanar Kashe kansa Matuƙar Atiku Abubakar Bai Biya Shi Bashinsa Ba
Wani Mutum Ya Hau Hasumiyar Sadarwa Don Neman Atiku Abubakar ya Biya shi Bashin Naira Miliyan 15. Da yake binsa.
A wani lamari da ya jawo hankalin jama’a, wani mutum ya hau saman wata hasumiyar sadarwa a Najeriya, yana barazanar kashe kansa a matsayin matakin nuna fushi.
Mutumin mai suna Musa Inuwa, ya ƙi saukowa daga hasumiyar duk da kokarin da ake yi na shawo kansa. Ya nace cewa sai an tilasta wa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, biyan sa Naira miliyan 15 da yake ikirarin cewa ana binsa sakamakon wani aiki da ya gudanar masa.
Rahotanni sun nuna cewa ya bayyana a fili cewa ba zai sauko ba sai dai idan ‘yan sanda sun shiga cikin lamarin su tabbatar an biya shi hakkinsa. Wannan mataki ya jawo cunkoso da tsayawar al’amura a yankin da lamarin ya faru, inda jami’an tsaro da masu aikin ceto ke ta kokarin lallashi da tabbatar da tsaron lafiyarsa.
Har yanzu dai ba a sami wani bayani daga bangaren Atiku ko wakilansa kan wannan zargi da mutumin ke yi ba.