
Rahotanni daga majalisar Dattijai dake Abuja na cewa, jami’an tsaro sun hana sanata Natasha Akpoti shiga cikin majalisar.
Dama dai tuni aka jibge jami’an tsaro a wajen majalisar Dattijai dan hana sanata Natasha Akpoti shiga majalisar.
Hakan na zuwane bayan da Sanata Natasha Akpoti ta sanar da cewa zata koma majalisar a yau, Talata biyo bayan hukuncin kotu da ya bata damar yin hakan.