A ci gaba da zargin karkatar da kudaden kasa da suka saka Najeriya cikin halin kaka nikayi, ana zargin kamfanin mai na kasa, NNPCL da karkatar da Naira Tiriliyan N2.68tn, da dala Miliyan $9.77m a cikin shekaru 4 da suka gabata.
Babban me binciken hada-hadar kudi na kasa ne yayi wannan zargi bayan kammala bincike akan yanda kamfanin na NNPCL ya gudanar da ayyukansa.
Tuni babban me binciken na kasa ya aikewa da majalisar tarayya da sakamakon bincikensa inda yace abinda kamfanin man na kasa, NNPCL ya aikata ya sabawa dokar kasa data haramta karkatar da kudaden kasa.
Duk da wadannan zarge-zargen, kamfanin man na kasa, NNPCL har yanzu yaki ya yi magana ko ya bayar da amsa akan zarge3da ake masa.