
Kamfanin samar da wutar Lantarki na kasa, TCN ya bayyana cewa, ya samar da wutar lantarki me karfin 5,801 megawatts wanda a Tarihin Najeriya ba’a taba samun wutar lantarki me karfin hakan ba.
Saidai ‘yan Najeriya dake amfani da wutar sun musanta wannan ikirari inda suka ce basu gani a kasa ba dan kuwa yankuna da yawa na kasar na kwana cikin duhu.
A ranar Alhamis ne dai shugaban hukumar a fadar shugaban kasa dake Abuja ya tabbatar da hakan.
Yace sun samu wannan nasara ne a ranar 4 ga watan Maris.
Yace kuma rassan kamfanin wutar na jihohi sun tura wutar gaba daya zuwa ga ‘yan Najeriya.