
Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa wasu yara 3 dake wanka a wani rafi dake kauyen Jinkiri na karamar hukumar Bauchi a jihar Bauchi sun rigamu gidan gaskiya.
Kakakin ‘yansandan jihar, Ahmad Wakili ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai ranar Laraba a Bauchi.
Ya bayyana sunaye da shekarun yaran da suka rasu kamar haka: Habibu Mohammed, 16, Abubakar Mohammed, 16, da Zailani Sule, 14, yace dukansu sun fito ne daga kauyen Durum.
Kuma sun rasu ranar Lahadi da misalin karfe 1 na rana.
Yace yaran na aikin hakar ma’adanai ne kamin zuwa su yi wanka, yace an yi kokarin kaisu asibiti amma akan hanya suka rasu kamin a karasa.
Yace likitoci sun tabbatar da mutuwar yaran kuma ana shirin mikasu wajan danginsu dan su binnesu.