Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi fatali da shawarar kwamitinsa na tattalin Arziki da suka ce masa kada ya aiwatar da kudirin gyaran haraji inda yace sai yayi.
Kakakin shugaban kasar,Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Ga abubuwa 13 game da kudirin dokar da ya kamata ku sani:
- Canja tsarin karbar haraji na mutum gudaguda ga ‘yan Najeriya a ciki da wajen kasar inda tsarin zai koma na zamani.
- Daina Karbar Haraji daga hannun masu fitar da kaya zuwa kasar waje dan karfafa fitar da kayan Najeriya zuwa kasuwannin Duniya.
- Daina karbar Haraji daga kananan ‘yan Kasuwa.
- Ba za’a karbi Haraji ba a hannun masu daukar Mafi karancin Albashi ba, sannan ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu za’a rage musu Haraji zuwa kaso 90.
- Ba za’a rika karbar haraji akan Abinci, Kiwon Lafiya, da Ilimi ba.
- Za’a baiwa kananan masu biyan haraji Kariya.
- Za’a ragewa kamfanoni Harajin da suke biya daga kaso 30 zuwa kaso 25 cikin 100.
- Idan Kamfani yayi asara ba zai biya Haraji ba.
- Za’a ragema kamfanoni Harajin VAT.
- Za’a hade duka haraji a waje daya ya zamana ana biyansa na bai daya maimakon daban-daban.
- Za’a yi raba daidai na Harajin VAT tsakanin jihohin da ke da kamfanoni da yawa da wadanda basu dasu.
- Sabon tsari dan Karbar Haraji ba da zalinci ba.