Thursday, December 26
Shadow

Karanta Jadawalin Alkawuran da Gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi wanda bata cikasu ba a shekarar 2024

A yayin da ya rage saura kwanaki kadan mu shiga shekarar 2024, mun kawo muku jadawalin alkawuran da Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta yi wadanda bata cikasu ba a wannan shekarar.

Alkawarin cire haraji akan kayan Abinci

Cire Haraji akan kayan Abinci dan samarwa talakawa hanyar saukin rayuwa abune da gwamatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta alkawarta ta bakin Ministan Noma, Abubakar Kyari.

Yace za’a cire haraji akan Alkama, Shinkafa, Masara da sauransu dan samarwa mutane saukin rayuwa.

A ranar 14 ga watan Augusta, Hukumar Kwastam ta sanar da izinin data samu daga fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dan cire tallafin.

Hukumar kwastam tace cire harajin zai fara aiki ne daga 15 ga watan July zuwa 15 ga watan Disamba.

Saidai da ba’a ga an cire harajin ba, an tambayi Hukumar Kwastam menene dalilin hakan inda tace tana jiran izinine daga ma’aikatar kudi.

Karanta Wannan  Matan mu na lalata da fararen hula saboda an kaimu daji yin yaki da 'yan bîndîgá an manta damu>>Sojojin Najeriya suka koka

Ministan kudi, Wale Edun ya yi zama na musamman da hukumar Kwastam kan lamarin amma yanzu da muke sauran kwanaki 6 shekarar ta kare har yanzu babu maganar cire harajin kuma ba’a bayyana sai yaushene za’a cire harajin ba.

Alkawarin Cire Haraji akan magunguna

Gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta yi Alkawarin cire Haraji akan magunguna da sauran kayan kula da lafiya da ake shigowa dasu daga kasar waje.

A ranar 28 ga watan Yuni ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa wata doka hannu wadda ta bayar da damar cire haraji akan magunguna da sauran kayan kula da lafiya da aka shigo dasu daga kasashen waje.

Ministan Lafiya da Walwala, Muhammad Ali Pate ya bayyana cewa, wannan mataki an daukeshine dan farfado da bangaren lafiya da kuma karfafa samar da kayan kula da lafiya a cikin gida Najeriya.

Watanni 4 bayan wancan Alkawari, karamin Ministan Lafiya da Walwala, Tunji Alausa ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta kammala aiwatar da kudirin dokar amma har yanzu magunguna sai kara tsada suke.

Karanta Wannan  Atiku Abubakar ƙyashi yake yi wa Shugaba Tinubu - Fadar Shugaban Ƙasa

Alkawarin rage farashin kayan masarufi.

A watan Janairu, Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso yayi alkawarin rage alkaluman hauhawar farashin kayan abinci zuwa maki 21.4 a karshen shekararnan ta 2024.

Saidai a bayanai na karshe da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar, tace a watan Nuwamba da ya gabata, makin tsadar farashin kayan abinci ya tashi zuwa 34.6 wanda rabon da aga hakan tun shekaru 28 da suka gabata.

Alkawarin Samar da katin dan kasa na musamman

A watan Afrilun da ya gabata ne dai gwamnatin tarayya ta sha Alwashin samar da katin dan kasa na musamman wanda zai rika baiwa masu shi damar cire kudi kamar ATM da sauransu.

Saidai har shekara ta kare gashi ba’a samar da katin dan kasar ba.

Karanta Wannan  Gwamnati ta karyata Lauyanta inda tace duka wadanda aka kama kananan yarane kuma za'a binciki jami'an tsaron da suka kamasu dan yi musu hukunci

Da aka tuntubi hukumar samar da katin dan kasa ta NIMC game da lamarin tace Gwamnati ba zata iya samar da kudin yin wannan katin dan kasa ba saidai duk wanda ke so ya biya kudi a yi masa.

Alkawarin Baiwa kananan hukumomi cin gashin kansu

A ranar 11 ga watan Yuli ne babbar kotu ta kasa ta yi hukuncin cewa Gwamnatin tarayya zata iya aikewa da kananan hukumomi kudaden shigarsu kai tsaye ba tare da bi ta hannun gwamnoni ba.

Hakanan kotun ta hana Gwamnati baiwa kantomomin kananan hukumomi kudaden shiga har sai an yi zabe an samu shuwagabannin kananan hukumomin.

Ranar 20 ga watan Augusta na shekarar nan da muke ciki, Gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti me mutane 10 wanda shine zai kula da aiwatar da wannan hukuncin kotu amma har zuwa yanzu kwanaki 6 suka rage mu shiga sabuwar shekara babu wannan batu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *