Friday, December 5
Shadow

Karanta Kaji:Sanatoci 3 kacal da suka ciri tuta suka ki amincewa da dokar dakatar da Gwamnan Rivers da shugaba Tinubu yayi

Sanatoci 3 ne kacal suka ciri tuta inda suka ki amincewa da dakatar da gwamnan jihar Rivers da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi.

A jiya ne dai majalisar dattijai data wakilai suka hada baki suka amince da dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa Gwamnan Rivers.

Saidai an bayyana sanatoci Seriake Dickson, da Enyinnaya Abaribe, da Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto a matsayin wadanda suka ki amincewa da wannan aniya ta shugaba Tinubu.

Rahoton yace wadannan sanatoci ficewa suka yi daga zauren majalisar kamin kakakin majalisar ya bayyana amincewa da kudirin.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Ji Abinda Dan shugaba kasa, Seyi Tinubu yace bayan da shugaban kungiyar daliban Najeriya yace yasa an masa dukan kawo wuka saoda yaki goyon bayan Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *