
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya koma Abuja daga nahiyar Turai bayan ziyarar aiki da ya kai biranen Paris da Landan.
Shugaba Tinubu ya isa filin jirgi na Nnamdi Azikwe da yammacin ranar Litinin, inda wasu manyan jami’an gwamnati suka tarbe shi.
A cewar fadar shugaban kasa, dalilan da suka sanya shugaban ya gudanar da wannan ziyarar sun haɗa da yin nazari kan wasu muhimman cigaban da gwamnatinsa ta samu.
”Zai yi amfani da wannan ziyarar domin yin nazari kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ke gudanarwa da kuma tsara yadda za a ɓullo da wasu sabbin shirye-shirye gabanin cikarsa shekara biyu kan karagar mulki,” a cewar fadar shugaban ƙasa.
A wani ɓangare kuma yayin da ake murnar samun ƙaruwa a asusun gwamnatin Najeriya na ƙasashen waje a babban bankin ƙasar, abubuwa da dama sun faru bayan fitar Tinubu daga Najeriya waɗanda suka tunzura wasu manyan ƴan siyasar ƙasar suka fara kira gare shi da ya koma gida.
Ƴansiyasa sun yi kira ga Tinubu da ya ‘dawo gida’
Ɗaya daga cikin ƴansiyasan da ya fara caccakar Bola Tinubu shi ne Peter Obi – ɗantakarar kujerar shugab ƙasa na jam’yyar Labour a zaɓen 2023.
Ya yi kira ga shugaba Tinubu da ya koma gida domin ya fuskanci matsalolin rashin tsaro da suka yi wa ƙasar dabaibayi.
Inda ya ce yana buƙatar ya jawo hankalin Shugaban ƙasar kan ƙalubalen rashin tsaro da mu ke fuskanta a gida, muna ya kuma yi kira gare shi da ya kawo ƙarshen ziyarra tasa cikin gaggawa.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar shi ma ya yi ƙorafi kan tafiyar da Tinubu ya yi, sakamakon matsalar tsaron da ke akwai a ƙasar.
Martanin da gwamnati ta mayar
Gwamnatin Najeriya dai ta mayar da martani kan waɗannan kiraye-kiraye inda sanarwar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce: ”Shugaba Tinubu yana gudanar da aikin shugabancin ƙasa duk da cewa yana Turai.
“Rashin kasancewarsa a ƙasar na wucin gadi ne kuma ya yi daidai da wa’adin lokacin da aka sanar na makonni biyu.”
Duk da cewa dai daga farko sun sanar da cewa shugaban zai yi makobiyu ne, daga baya ziyarar tasa ta ɗauki kwanaki 18.
Abubuwan da suka faru
A cikin sama da mako biyu da Shugaba Tinubu ya yi a ƙasashen waje, wasu muhimman abubuwa sun afku a wasu jihohin ƙasar:
Jihar Filato:
- Ƴanbindiga sun kashe mutane 50 a ƙaramar hukumar Bassa a ranar 14 ga watan Afrilu.
- Gomman mutane sun rasa rayukansu a wani hari da aka kai a wasu ƙauyuka na jihar.
- Wani harin ƴan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane 52 a ƙaramar hukuma Bokkos
Jihar Benue:
- Na kashe mutane 56 a wani hari da aka kai yankunan Logo da Gbagir da ke ƙaramar hukumar Ukum.
Jihar Borno:
- Rahotanni sun ce mayaƙan Boko Haram da ISWAP sun ƙwace iko da yankunan wasu ƙananan hukumomi a jihar da suka haɗa da Gudumbari da Marte da Abadam.
- Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya koka kan cewa hare-haren Boko Haram da na ISWAP na ƙariuwa a Jihar.
Jihar Ribas:
- An gudanar da zanga-zangar adawa da kuma goyon bayan ayyana dokar ta-baci da shiugaba Tinubu ya yi a jihar.