
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyanawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cewa ya daina sauraren masu zaginsa.
Yace ana samun canji sosai kuma na Alheri sanadiyyar salon mulkinsa.
Ya bayyana hakane a jawabin da yayi a wajan taron kaddamar da gyaran da akawa babban dakin taro na Abuja.
Akpabio yace ko da mutane naso ko basa so, majalisar tarayya tana Alfahari dashi.