KARON FARKO: Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ziyarci Babban Masallacin Sheikh Zayyad da ke Abu Dhabi, wanda ke ɗaya daga cikin manyan masallatai a duniya mai cike da fasahar gini ta zamani.

Trump ya ziyarci masallacin ne a yayin ziyararsa zuwa babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Ya samu rakiyar Sheikh Khaled bin Mohamed, Yarima Mai Jiran Gado na Abu Dhabi.