
Hadimin shugaban kasa, Tope Fasua ya zargi matashiya me bautar kasa, ‘Raye’ Uguamaye da cewa Karuwancine ya kaita jihar Legas.
Wannan zargi nashi na zuwane bayan da sunan matashiyar ya yadu sosai a kafafen sadarwa bayan da ta soki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Tope yace matashiyar ta je legas ne dan samun rabonta na Naira Biliyan N661.
Kwanannan ne aka bayyana cewa mazan Legas sun kashe Naira Biliyan N661 wajan biyan bukatarsu da karuwai.
A baya dai, wani hadimin shugaban kasar me suna Temitope Ajayi ya nemi a kaddamarwa matashiya Raye da hukuncin kisa saboda sukar shugaban kasar.
Saidai daga baya ya fito ya bayyana cewa, shi ba haka yake nufi ba.