Monday, April 21
Shadow

Wasu na ta tambayar wai Ina Kwankwasone, kowane babban dan Adawa yayi Allah wadai da dakatar a Gwamnan Rivers amma har yanzu shi bai ce komai akai ba

A yayin da siyasar Najeriya ta mayar da hankali kan dakatar da gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara, manyan ‘yan Adawa na ta Allah wadai da wannan mataki na shugaban kasa.

Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasiru El-Rufai, da sauran manyan ‘yan Adawa duk sun fito suna ta Allah wadai da wannan mataki, saidai ba’a ji duriyar Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ba.

Daya daga cikin wadanda suka bayyana irin wannan ra’ayi shine Comrade Adnan.

Ya bayyana cewa, duk da shirun Kwankwaso akan lamari irin wannan amma haka mutane ke kiransa da Jagora.

Abin dai jira a gani shine ko Kwankwaso zai yi magana akan lamarin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda aka kama wata me sayar da abinci na fitsari a cikin tukunyar miyar abincin da take sayarwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *