
Tsohon ministan Sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya bayyana cewa, yana nan a APC bai koma jam’iyyar hadakar ‘yan Adawa ta ADC ba.
Ya bayyana hakane ta shafinsa na X.
Sirika yace abin ya bashi mamaki da yaji Wike na cewa, wai ya koma ADC hakanan kuma sai ya ji me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga shima yana cewa ya Koma ADC.
Yace kasancewarsu manyan mutane bai yi tsammanin zasu rika yada labarin da bashi da inganci ba.
Yace duk inda Buhari yake shima yananan dan haka bai bar jam’iyyar APC ba.