Thursday, April 16
Shadow

Karya ake min ban taba yin sana’ar Sayar da katin waya ba>>Inji Tsohon Hadimin Buhari, Malam Bashir Ahmad

Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya mayar da raddi bayan da wani yace a da kamin ya shiga harkar siyasa yna sana’ar sayar da katin waya ne.

Malam Bashir Ahmad ya bayar da tallafin Naira Miliyan 5 ne a wani shiri da ake yi na tara kudaden da za’a tallafawa matasa da sana’o’i a Arewa.

Sai wani yace a da fa sana’ar sayar da katin waya yake.

Saida malam Bashir Ahmad ya karyata wannan ikirari.

Yace idan da yayi sana’ar sayar da katin waya ba zai ji kunyar fadar hakan ba da itama sana’a ce kuma wasu sun yi sun samu nasara a rayuwa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Sheikh Aminu Daurawa Dan Shi'a ne shiyasa yake cewa awa kasar Iran Addu'a amma baya halatta ga Musulmi na kwarai yawa kasar Iran addu'ar>>Inji Sheikh Saidu Aliyu Maikwano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *