
Gwamnatin tarayya ta karyata wani rahoton jaridar Daily Trust wanda yace akwai yunwa a Arewa inda suka ce mutane miliyan 33 na fama da yunwa ciki akwai miliyan 16 wadanda kananan yara ne
A wata sanarwa da ta samu sa hannun me magana da yawin shugaban kasa tace Gwamnatin ta rabawa gidaje Miliyan 3 tallafin Naira 75,000 kowannensu.
Sannan kuma akwai dalibai 396,000 da suka samu tallafin karatu.
Sannan akwai kananan masana’antu da suka samu tallafin jari.
Fadar shugaban kasar tace tana maraba da suka me ma’ana amma a rika fadar kokarin gwamnati.