
Sanata Godswill Akpabio kakakin majalisar dattijai ya bayyana cewa, Karya sanata Natasha Akpoti ke masa da tace ya nemi yin lalata da ita.
Ya bayyana hakane a zaman majalisar na ranar laraba.
Inda yace shi bai taba cin zarafin kowace mace ba a rayuwarsa ya kara da cewa shi har kyautar girmamawa aka bashi saboda kare hakkin mata.
Sanata Natasha Akpoti dai ta zargi kakakin majalisar dattijan da neman yin lalata da ita shiyasa baya bata damar gabatar da ayyukan ci gaba a majalisar.