Sunday, March 23
Shadow

Karyace:Fubara ya mayarwa da shugaba Tinubu martani bayan da yace bai tabuka komai ba yayin da aka kaiwa Bututun man fetur din Najeriya hari

Gwamnan jihar Rivers da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar, Simi Fubara ya bayyana cewa ba gaskiya bane ikirarin da shugaban kasa yayi na cewa bai tabuka komai ba kan matsalar tsaron da ta kunno kai a jihar.

Ya kuma karyata ikirarin shugaban kasar na cewa ya rushe majalisar jihar Rivers ba tare da gina wata ba.

A martanin da ya mayar ta hannun me magana da yawunsa,Nelson Chukwudi Gwamna Fubara ya bayyana cewa, abin mamakine fadar shugaban kasar na magana akan abinda basu da masaniya akansa.

Yace ko da yake ya dora Alhakin hakan akan masu baiwa shugaban kasar bayanai wanda sune suka kasa bashi bayana da ya kamata yayi amfani dasu wajan yin shawara.

Karanta Wannan  Dogarin Sanata Barau Jibrin ya rasu

Fubara yace maganar da tsohon gwamnan jihar, kuma ministan Abuja a yanzu, Nyesome Wike yayine tasa aka kai harin.

Yace Wike a bayanin da yayi ya ce ba Kabilar Ijaw basu ne kadai zasu iya fasa bututun man fetur ba, ikwerre ma zasu iya yi, sannan ya bayyana kabilar Ijaw da cewa marasa rinjayene a siyasar Najeriya.

Fubara yace Kabilar Ijaw ta yi kira game da Wike ya janye wannan magana tasa kuma ya basu hakuri amma yaki.

Yace shi kuma a nashi bangaren tun da ya zama gwamna yake ta kokarin ganin ya samar da zaman lafiya a jihar, yace ya bayar da kyautar motoci, da jiragen ruwa da sauran kayan aiki ga jami’an tsaro.

Karanta Wannan  Bamu yadda ba zamu je kotu, Kungiyar Kiristoci kan hutun Ramadan da jihohin Arewa suka bayar a makarantu

Yace ta yaya kuma za’a ce bai tabuka komai wajan samar da tsaro a jihar ba.

Yace maganar sake gina Majalisar jihar Rivers kuma, tun Wike yana gwamna yasan cewa majalisar har zubar da ruwa take kuma ‘yan majalisar sun nemi ya sake gina musu wata ta zamani amma yaki.

Yace amma shi yana zama gwamna ya dauki aniyar gyaran majalisar dalili kenan da yasa ya rusheta kuma aka fara ginin wata.

Yace dan haka duka ikirarin na shugaban kasa ba gaskiya bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *