Kasar Afghanistan ta yi sabuwar dokar hana mata tsayuwa kusa da taga.
A sabuwar dokar, ba’a yadda mace ta tsaya ko ta zauna a kusa da taga ba.
Hakanan an bayar da dokar toshe tagogin gidaje dake fuskantar gidan makwabta.
Dokar ta zo ne a wani yunkuri da kungiyar Taliban dake mulkar kasar ke yi na kiyaye hakkin mata.