
Kasar Amurka ta sanar da cewa, duk dan Chiranin dake kasar ta amince zata bashi dala $3000 kwatankwacin sama da Naira Miliyan 4.3 kenan idan ya yadda ya koma kasarsa.
Kasar ta bayyana hakane daga Ma’ikatar DHC inda a baya dala $1000 ce kawai ake baiwa ‘yan Chiranin idan sun amince zasu koma kasashen nasu.
Hukumar tace daga watan Janairu na shekarar 2025 zuwa yanzu ‘yan Chirani akalla Miliyan 1.9 suka amince su koma kasashen su daga kasar Amirkar ba tare da an kamasu ba.