
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Burkina Faso ta samu kudin shiga da suka kai Dala Biliyan $18 tun bayan da Ibrahim Traore ya zama shugaban kasa a shekarar 2022.
Bayan da ya zama shugaban kasa, Ibrahim Traore ya kwace kamfanonin hakar ma’adanai na turawa inda ya mayar dasu mallakar kasar ta Burkina Faso.
Hakan ya taimaka sosai wajan kara yawan kudin shigar da kasar ke samu daga Gwal.
A baya, kamin ya zama shugaban kasa, Kasar ta Burkina Faso na samun kudin shiga Dala Biliyan $1 ne kacal daga sayar da Gwal.
A shakerar 2024, kasar Burkina Faso ta fitar da Ton 60 na Gwal.