
Rahotanni daga kasar Ghana na cewa, kasar ta koro ‘yan Najeriya 42 da suka je chirani kasar.
Kasar ta kori jimullar ‘yan kasashen waje 68 daga yankin Ashanti bayan da aka samesu da aikata miyagun laifuka, irin su Qaruwanchi, da sauransu.
Hukumomin kasar sun ce sun dauki wannan mataki ne dan tsaftace kasarsu da kuma kiyaye al’ummarsu daga miyagun laifukan da bakin ciranin ke yi.