
Rahotanni daga kasar Ingila na cewa, kasar na fama da karancin aikin yi wanda rabon da aga irin sa shekaru 4 kenan da suka gabata.
Hakanan rahoton yace ma’aikata basa samun karin Albashi yanda ya kamata.
Alkaluma daga hukumar kididdigar kasar, (ONS) sun bayyana cewa rashin aikin yin ya karu da kaso 4.5 cikin 100 wanda rabon da aga hakan tun shekarar 2021.