Saturday, June 27
Shadow

Obasanjo da Atiku da Obi sun halarci kaddamar da littafin Sule Lamido a Abuja

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, tsofaffin Mataimakan Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da Namadi Sambo, da tsofaffin Shugabannin Majalisar Dattawa, Ken Nnamani da Pius Ayim, sun isa wurin kaddamar da littafin tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido.

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, shi ne zai yi nazari kan tarihin rayuwar Lamido da ke dauke da take “Being True to Myself”.

Daga cikin manyan baki da suka halarci kaddamar da littafin a cibiyar taro ta NAF da ke Abuja har da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, sai gwamnonin Gombe, Muhammadu Yahaya; Jigawa, Umar Namadi; da na Filato, Caleb Mutfwang.

Karanta Wannan  Ban san ta yaya suke iya bacci ba yayin da 'yan tà'àddà ke kàshè mutane>>Atiku ya koka kan matsalar tsaro, yace shuwagabannin da suka zo bayan mulkinsu shi da Obasanjo ne suka kawo matsalar tsaro

Haka zalika, wasu daga cikin fitattun mutane da suka halarta sun hada da tsofaffin gwamnonin Benue, Gabriel Suswam; Kaduna, Ahmed Makarfi; Neja, Babangida Aliyu; da na Cross Rivers, Liyel Imoke, da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *