
Kasar Iran tace bata aminta da sharudan da kasar Amurka ta gindaya mata na maganar sulhun makamin kare dangin da take son mallaka ba.
Iran tace ita kasa ce me cin gashin kanta dan haka ba zata saurari Amurka ta bata sharadi akan yanda zata gudanar da kasarta ba ko makamin kare danginta ba.
Iran tace idan dai ana son tattaunawar ta ci gaba, to itace zata gindaya sharudan da za’a bi wajan ci gaba da tattaunawar.