Wednesday, January 15
Shadow

Kasar Libya na kama ‘yan Najeriya dake zaune a kasar da kakaba musu haraji me yawa saboda Haushin Najeriya da suke ji kan wasan kwallon kafa da basu yi nasara ba

Rahotanni daga kasar Libya na cewa hukumomi a kasar na yiwa ‘yan Najeriya dake zaune a kasar kamun kan mai uwa da wabi da kakaba musu haraji me yawa dan Huce haushi.

Najeriya dai ta yi nasara akan kasar Libya ne bayan da Najeriyar ta kai karar kasar Libya kan cin zarafin da tawa ‘yan wasan Super Eagles.

Hukumar kwallon kafa ta Africa CAF ta baiwa Najeriya gaskiya inda ta baiwa Najeriya maki 3 sannan ta ci kasar Libya tarar Dala $50,000.

Najeriya dai ta je kasar Libya ne dan buga wasa zagaye na biyu na neman shiga gasar cin kofin nahiyar Africa.

Karanta Wannan  Kalli Kayatattun hotunan Rahama Sadau

Saidai hukumomi a kasar ta Libya sun karkatar da jirgin ‘yan wasan Najeriyar zuwa wani gari na daban dake da nisa da wajan da za’a yi wasan.

Hakanan an ki baiwa ‘yan wasan Najeriyar motar da zata kaisu garin da zasu yi wasan kuma Gwamnatin Najeriya ta samarwa ‘yan Wasan Najeriyar motar da zata kaisu wajan wasan amma duk da haka aka hanasu fita daga filin jirgin.

Hakan yasa hukumar kwallon kafa ta NFF ta Najeriya ta cewa ‘yan kwallon Najeriya su dawo gida kada su buga wasan inda daga baya ta shigar da korafi gaban hukumar kwallon kafa ta Africa CAF kuma ta yi nasara.

Karanta Wannan  Ya kamata Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji - NLC

Lamarin bai yiwa kasar Libya dadi ba inda hakan yasa ta koma kamen ‘yan Najeriya ba gaira babu dalili da kuma kakaba musu haraji me yawa.

Tuni dai shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Libyan, Nasser Al-Suwai’I ya bayyana hukuncin da cewa ba’a yi adalci ba inda yace zasu daukaka kara.

Yayi zargin cewa Najeriya na da uwa a gindin murhu ne a wajan hukumar kwallon kafar ta kasar Libya shiyasa aka bata gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *