Sunday, December 14
Shadow

Kasar Nijar ta koro ‘yan Najeriya 148 da suka shigar mata kasa ba bisa ka’ida ba

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta bayyana cewa ta karbi ‘yan Najeriya su 148 da kasar Nijar ta dawo dasu gida saboda shiga kasarta ba bisa ka’ida ba.

Hukumar tace ranar Talatace aka dawo da ‘yan Najeriyar a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Legas.

Hukumar tace 120 daga cikinsu maza ne manya inda guda 9 mata ne manya sai, sai guda 10 yara ne maza, sai 7 yarane mata, sai jarirai 2.

Karanta Wannan  Matsalar tsaron Najeriya bata yi munin da za'a ce mutane su fara tashi suna kare kansu ba>>Inji Gwamnan jihar Jigawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *