Rahotanni sun bayyana cewa, kasashen Larabawa sun dauko alwashin ba zasu sake barin Falas-dinawa au mallaki makamai ba bayan an gama yaki tsakaninsu da Israela.
Hakan na zuwa ne yayin da ake tsammanin za’a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Israela da Kungiyar Hamas.
Saidai abin tambaya anan shine, anya kasashen Larabawan zasu iya aikata hana Falas-dinawa mallakar makamai?
Dalili kuwa shine a yanzu gashi ana ta kashesu babu kasar Larabawan data shigar musu ko ta tsaya musu, an zura ido ana kallo Israela na musu kisan kare dangi, ta yaya zasu yadda a hanasu mallakar makamai bayan sun san duk randa Israela ta sake far musu da yaki babu me tare musu?
Wannan dai abune me kamar wuya.