
Dan Gwagwarmaya kuma dan siyasa, Mawallafin Jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, Sojojin Ruwan Najeriya kaso 35 cikin 100 ne kawai na ruwan Najeriya suke iya tsarewa.
Ya bayyana cewa, sauran wasu kamfanoni ne masu zaman kansu aka baiwa suke kula da tsaron ruwan kasar.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi inda yake magana akan gazawar jami’an tsaron Najeriya.