Tuesday, May 19
Shadow

Mun gana da Kiristoci da ke zaune a sansanin ‘yan gudun Hijira ba zamu kyale Fulani da suka sakasu a wannan halin ba dole mu dauki mataki akansu>>Inji ‘yan majalisar kasar Amurka da suka kawo ziyara Najeriya

Yan majalisar kasar Amurka da suka kawo ziyara Najeriya wanda Riley Moore ya musu jagora sun ce sun gana da Kiristoci da aka yiwa cin zarafi a jihar Benue.

Sun ce sun gan su a matsayi na rashin tabbas wanda suka zargi Fulani da jefasu a ciki.

Riley yace ba zasu zuba ido suna ganin irin wannan abuba, dole zasu dauki mataki.

Yace ya ji labarai masu tayar da hankali da ‘yan Gudun Hijirar suka gaya masa wadanda ba zai taba mantawa dasu ba.

Karanta Wannan  Ya kamata shuwagabannin Najeriya su yi koyi da halin marigayi Fafaroma na son Talakawa>>Inji Jam'iyyar NNPP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *