Sunday, January 26
Shadow

Kaso 77 na matan Najeriya na Amfani da man kara hasken fata>>Inji WHO

Kungiyar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana cewa, kaso 77 cikin 100 na matan Najeriya na amfani da man kara hasken fata wanda ake cewa Bleaching.

Hakan bmna zuwane yayin da wani rahoto yace ba matan ba kadai yanzu hadda kananan yara a Najeriya ana shafa musu man kara hasken fata.

Rahoton na WHO yace mayukan kara hasken fata ne mafiya ci gaba da aka fi sayarwa a tsakanin mayukan shafawa a Duniya baki daya.

Hakan na faruwa ne duk da irin illar da irin wadannan mayukan shafawar ke dauke da ita wanda ya hada da ragewa fata karfi da garkuwar da take dashi da kuma kara hadarin kamuwa da cutar daji.

Karanta Wannan  Hotunan Sabon Jirgin Saman Shugaban Kasa Bola Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *