
Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa, kaso 90 na musulman Najeriya Sunni ne.
Ya bayyana hakane a martanin da yakewa ‘Yar siyasar kasar Canada, Goldie Ghamari inda tace Najeriya na hada kai da kasar Iran dan Khasye Kiristoci.
Yace abinda ma bata sani ba shine kaso 90 na musulman Najeriya Sunni ne.
Yace ‘yan kasar waje suna amfani da rarrabuwar mu ne wajan cimma burinsu inda yace sai mun hada kai.