
Matar tsohon Shugaban kasa, Patience Jonathan bayan ta kammala karatun Digiri na 3 watau PhD ta bayyana irin wahalar da ta sha.
Ta bayyana hakane a wajan taron cocin Streams of Joy International Church.
Tace a lokacin da ta je sayen fom din fara karatun ta rika kokwanton ko zata iya, shin me ma zata yi da wannan karatun tunda da ta zama har matar shugaban kasa?
Tace amma ta karfafa kanta inda tace idan ‘ya’yanta zasu iya to itama zata iya.
Tace malamai idan ta kai musu aikinta sai su rika ce mata taje ta gyara guri kaza da kaza, tace hakan yana sa ta tambayi cewa shin wadannan basu san cewa ta tsufa ba?
Tace a haka dai Allah ya taimaketa ta kammala karatun.