
Sanata Ahmad Ningi ya bayyana cewa, Bai taba Tunanin cewa wata rana za’a wayi gari a janyewa Sanatoci jami’an tsaron ‘yansanda dake basu kariya ba.
Yace abin takaici shine ga mawaka, ‘ya’yan ‘yan siyasa, da sauran wadanda basu kamata ba har yanzu ‘yansanda na take musu baya.
Yace indai an janye musu masu take musu baya, to kamata yayi suma Gwamnoni da Ministoci da shugaban kasa duk a janye musu masu take musu baya.