Ko Kudin Asusun Gwamnatin Kano Kwankwaso Ya Wawushe Baki Daya, Mu Kanawa Mun Yafe Masa, Inji Aisha Muhammad Adam
A madadina da kuma sauran ragowar al’ummar jihar Kano ta dabo na zo na ari bakin kowa na ce albasa domin mika sako izuwa ga Maigirma Kwankwaso Madugu Uban Tafiya, Dan Musa Gagara Badau, cewa mu mutanen jihar Kano mun yafe maka koda a ce ka ci wannan kudin da ake fada ka ci, to mu mun yafe. Ka ci bagas, ka ci halak malak.
Ai dama dukiyar ta mu ce mu kuma naka ne, to kaida kaya duk mallakar wuya ne.
Yau a ce koda asusun gwamnatin Kano ka wawushe ka bar shi babu ko kwandala to mun yafe kasha kuruminka. Muna tare da kai, babu wanda za mu bari ya tozarta ka.
Kanawa me za ku ce?