Friday, December 5
Shadow

Kotu ta aikawa bangaren su David Mark sammace akan shugabancin jam’iyyar ADC

Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta aikawa shugaban jam’iyyar ADC na riko, David Mark takardar sammace inda tace ya je ya kare kansa akan shugabancin jam’iyyar.

Motun ta bukaci David Mark da sakataren riko na jam’iyyar ADC, Rauf Aregbesola su je su gaya mata dalilan da zasu hana a tsigesu daga shugabancin jam’iyyar.

Hakan na zuwane bayan da Nafiu Gombe ya gabatar da kara a kotun inda yake cewa shine halastaccen shugaban jam’iyyar ADC ba David Mark ba.

Ya kuma bukaci kotun data tsige David Mark daga shugabancin jam’iyyar ADC.

Saidai kotun bata amsa bukatarsa ba inda tace maimakon tsige David Mark, tana bukatar ya bayyana a gabanta kamin 15 ga watan Satumba dan ya bata hujjojin da zasu sa kada a tsigeshi daga shugabancin jam’iyyar ADC.

Karanta Wannan  Wani bawan Allah ya baiwa Amani Kyautar Naira Miliyan 2, Fadila H Aliyu ta sha Alwashin riketa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *