Friday, December 5
Shadow

Kotu ta bayar da belin Mahadi Shehu kan Milyan uku

Wata babbar kotun jihar Kaduna ta bayar da belin mai fafutuka Mahdi Shehu kan kudi Naira miliyan uku da kuma mutane biyu da za su tsaya masa a kan wannan kudi.

Kotun ta ce wadanda za su tsaya wa dole ne su zama sanannun malamai a Nageriya.

Sannan ta kwace fasfonsa kuma tace dolene sai ya rika zuwa wajan jami’an tsaro duk wata ana ganinsa, kuma duk idan ya zama dole sai yayi tafiya, ya sanar da kotun.

Kotun tace ta amince ta bayar da belinsa ne saboda a yanzu ba’a tabbatar da laifin daya aikata ba.

Karanta Wannan  " Jita-jitar da ake yi kan komawa ta APC gaskiya ne. Ni dama siyasata ta mutane ce. Kare muradun al'ummar da nake wakilta shi na sa a gaba…," Kawu Sumaila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *