Kotun tarayya dake Abuja ta bayar da belin matar datawa dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da shugaban ‘yansandan Najeriya barazanar kisa akan Naira Miliyan 10.
Alkalin kotun, Justice Emeka Nwite ya bayyana cewa kuma matar da aka gurfanar Olamide Thomas sai ta gabatar da wanda zai tsaya mata.
Kuma dole ya kasance yana zaune a inda kotun ke da hurumi.