
Kotun tarayya dake da zama a Abuja ta amincewa hukumar EFCC ta ci gaba da rike kadarorin tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami.
Kotun tace EFCC ta rike kadarorin guda 57 na wucin gadi kamin a amince a kwacesu na dindindin.
Hakanan Kotun ta bayar da belin Malami da dansa da matarsa.
Hakanan a zaman kotun, Mai Shari’a, Justice Emeka Nwite ya Gargadi Lauyan Abubakar Malami cewa kada ya sake yace zai nemi wata Alfarma a wajansa.
Yace ba zai lamunce a bata masa suna ba kuma duk sanayyarsa da mutum idan aka zo wajan aiki zai nuna ba sani ba sabo.