Tuesday, February 10
Shadow

Kotu ta bayar da Umarnin EFCC ta rike kadarorin Abubakar Malami 57

Kotun tarayya dake da zama a Abuja ta amincewa hukumar EFCC ta ci gaba da rike kadarorin tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami.

Kotun tace EFCC ta rike kadarorin guda 57 na wucin gadi kamin a amince a kwacesu na dindindin.

Hakanan Kotun ta bayar da belin Malami da dansa da matarsa.

Hakanan a zaman kotun, Mai Shari’a, Justice Emeka Nwite ya Gargadi Lauyan Abubakar Malami cewa kada ya sake yace zai nemi wata Alfarma a wajansa.

Yace ba zai lamunce a bata masa suna ba kuma duk sanayyarsa da mutum idan aka zo wajan aiki zai nuna ba sani ba sabo.

Karanta Wannan  Ya kamata Amaechi da Atiku su hakura da tsayawa takarar shugaban kasa a ADC su barwa matasa>>Inji Hakeem Baba Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *