
Kotu dake Normansland a Kano ta daure mutane 2 bisa hannu a sare itace a jihar wanda sabawa dokar Muhalli ta jihar ne.
Ma’aikatar Muhalli ta jihar, ta sanar da cewa an kama wani me suna Salihu Mukhtar da wani abokin aikinsa da suka sare itace akan titin Jigawa Road dake Nasarawa GRA.
Lauya me gabatar da kara, Barrister Bahijjah Aliyu ne ya gayawa kotu cewa wadanda aka kama din sun karya dokar muhalli ta jihar.
An yankewa daya daga cikinsu hukuncin daurin watanni 3 a gidan yari ko biyan tarar Naira 20,000.
Sannan aka yankewa dayan hukuncin daurin watanni 6 a gidan yari ko biyan tarar Naira dubu 50.
Kwamishinan muhalli na jihar, Dr. Dahiru Hashim ya bayyana cewa ba zasu amince da sare itatuwa a jihar ba.