
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gayawa tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya hakura da maganar rasa mukamin minista wadda an yi tun tuni.
Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga inda yace El-Rufai sai raki yake kamar wani karamin yaro da aka kwacewa biredi.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na ChannelsTV.
Onanuga yace kamata yayi El-Rufai ya sakawa ransa dangana ya bar maganar rasa mukamin ministan da yayi.
Onanuga yace yana tausayawa El-Rufai dan ya ga Alamar lamarin ya bata masa rai sosai.
A jiya ne dai El-Rufai a hirarsa da Arise TV ya bayyana cewa, Tinubu ne ya ki bashi minista ba Majalisa ce ta ki amincewa dashi ba.