Babbar Kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta hana babban bankin Najeriya, CBN ci gaba da turawa jihar Rivers kudadenta na shiga da gwamnatin tarayya ke aikawa kowace jiha.
Mai Shari’a, Joyce Abdulmalik ce ta yanke wannan hukunci bisa dalilin cewa gwamnan jihar Sim Fubara baya bin doka wajan kashe kudaden da ake turawa jihar.
Dan hakane tace kada a sake turawa jihar wadannan kudade.
Wasu masu sharhi da yawa dai sun bayyana wannan mataki da cewa ba ya rasa nasaba da rashin jituwa dake tsakanin Gwamna Sim Fubara da Nyesome Wike.