Saturday, March 22
Shadow

Kotu ta hana INEC shirya zabe dan yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye

Rahotanni sun bayyana cewa, babbar Kotun tarayya dake Lokoja ta hana yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye.

Kotun tace kada hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta sake ta amince da bukatar shiryawa sanata Natasha Akpoti kiranye.

Wani me suna Anebe Jacob Ogirima ne da wasu mutane hudu daga mazabar ta Sanata Natasha Akpoti suka shigar da bukatar a gaban kotun.

Mai shari’a Justice Isa H. Dashen ta amince da bukatar tasu.

Sannan an dage sauraren karar sai nan da 6 ga watan Mayu.

A baya dai Bidiyo da hotuna aun bayyana na mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti inda aka ga ana shirya zaben yi mata kiranye.

Karanta Wannan  Yaro daya ya Mùtù wasu 21 sun jikkata bayan da tukunyar gas ta fashe a Goron Dutse, Kano

Sanata Natasha Akpoti ta fara samun matsala ne tun bayan da ta zargi kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio da neman ta da lalata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *