
Kotun tarayya dake Abuja ta ki amincewa da bukatar Gwamnatin tarayya ta kama dakatacciyar sanata Natasha Akpoti.
Gwamnatin na son a kama Sanata Natasha Akpoti ne saboda kun ta ki bayyana a kotu wajan shari’ar da ake yi ta zarginta da bata suna.
Mai shari’a, Justice Muhammed Umar ne ya yanke wannan hukunci bayan da lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe, ya nemi a kama Sanata Natasha Akpoti saboda kin halartar kotun duk da cewa an baiwa Lauyanta Sammace.
Saidai Mai Shari’a Muhammad Umar ya bayyana cewa, tunda ba Sanata Natasha Akpoti da kanta aka baiwa samacen ba ba za’a iya cewa lallai ta samu sammacen ba.
Dan haka ya daga ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Yuni.