Friday, December 5
Shadow

Kotu Ta Tasa Keyar Wasu Mutane Biyar Zuwa Gidan Yari A Kano Saboda Awakinsu Sun Ci Shukar Gwamnati

Kotu ta yanke wa mutane biyar hukunci bisa sakin awaki su lalata bishiyu a Kano.

Wata kotun majistare da ke Kano ta yanke wa mutane biyar hukuncin daurin wata guda a gidan yari saboda barin awakinsu su yi yawo babu kulawa tare da lalata shuke-shuken ado da gwamnatin jihar ke yi a titunan Lodge Road da Race Course Road.

Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ce ta gurfanar da wadanda aka kama, karkashin jagorancin Usman Abdullahi, bisa sashe na 7(e) na dokar lafiyar jama’a ta jihar Kano ta shekarar 2019, wadda ke haramta duk wani aiki da zai lalata kayayyakin more rayuwa na gwamnati ko ya zama barazana ga muhalli.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Likafa ta yi gaba inda aka ga Iftihal Madaki a karo na biyu tana rawa da Soja Boy

LEADERSHIP ta rawaito cewa lamarin ya jawo hankalin jama’a makonni da suka gabata bayan jami’an ma’aikatar sun kama awaki 17 da aka samu suna kiwo a cikin shuke-shuken ado da gwamnati ke kula da su.

An mika awakin ga ‘yan sanda a matsayin wani bangare na kamfen da ake yi don kare ayyukan gyaran gari daga barna da cin zarafin muhalli.

A yayin zaman kotun, lauya mai shigar da kara, Barrista Bahijjah Aliyu, ta bayyana cewa awakin mallakin mutanen biyar din da ake tuhuma ne, kuma sun yi mummunar barna ga shuke-shuken da aka tanada don inganta muhalli.

Kotun ta same su da laifi, tare da ba su zabin biyan tarar naira dubu 25 kowannensu a maimakon zaman gidan yari na wata guda.

Karanta Wannan  Karanta Jadawalin mutane 9 da zasu yi takara da Sheikh Isa Ali Pantami wajan neman takarar Gwamnan jihar Gombe a shekarar 2027

Haka kuma, kotun ta umarce su su hada su biya naira dubu 100 a matsayin diyya kan barnar da aka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *