
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa Amurka bata isa ta kawo Hari Najeriya ba sai da amincewarsa.
Ya bayyana hakane ta bakin me bashi shawara kan sadarwa, Daniel Bwala a hirarsa da manema labarai.
Daniel Bwala yace Keta dokar kasa da kasa ne wata kasa ta kaiwa wata kasa hari ba tare da sanin kasar da aka kaiwa harin ba.
Yace ba’a fahimci abinda Trump ya fada bane, wannan abu ne da zasu warwareshi ta hanyar Diplomasiyya.
Ya bayyana cewa, Suna godiya ga Trump da amincewa da yayi ya sayarwa da Najeriya makamai a zamanin mulkinsa na farko.