
Dan takarar mataimakin shugaban kasa a shekarar 2023 karkashin jam’iyyar Labour Party, Datti Babba Ahmad ya bayyana cewa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai cika Alkawuran da ya daukarwa ‘yan Najeriya ba.
Yace dalili kuwa an tabbatar cewa jam’iyyar APC ta shugaban kasar, makaryaciyace.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Arise TV.
Datti Baba Ahmad ya kara da cewa, Ya hango kamin zaben 2027, ‘yan Najeriya zasu hada kai kuma jam’iyyar APC zata fadi zabe.