
Babban lauyan Gwamnati, Lateef Fagbemi ya kare matakin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dauka na dakatar da gwamnan jihar Rivers.
Inda yace shugaban kasar na da karfin ikon dakatar da kowanw Gwamna.
Fagbemi ya gargadi gwamnonin cewa duk gwamnan dake neman zama barazana ga Gwamnatin Tinubu na iya fuskantar dakatarwa.
Yace a yau gwamnan jihar Rivers ne a gobe zai iya zama kowane Gwamna.
Ya gargadi cewa babu wanda zasu bari ya mayar da Dimokradiyya abin wasansa.